Rundunar Yan Sandan jahar Kano, ta Gurfanar da Wani matashi Mai suna Murtala Sa’idu Tudun Murtala, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci ta Fagge Kano, karkashin jagorancin Mai shari’a Umar Lawan Abubakar, bisa kunshin tuhumar tayar da haniya da Yunkurin aikata laifi.
Ana zargin matashin da zuwa Wani Asibiti dubiya Amma ya Kai wa mara lafiyar kwayoyi ma su Sanya maye, Inda aka kama shi lokacin da yake Yunkurin ba shi.
Mai gabatar da kara Zaharaddin Mustapha, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake Yi masa, Inda nan ta ke ya amsa laifinsa, kuma kotun ta kafa masa shaidun Jin ikirari.
Alkalin kotun Mai shari’a Umar Lawan Abubakar, ya yanke masa hukuncin daurin shekara Daya ko biyan tarar naira Dubu arba’in da Bulala 30.
Haka zalika an yanke masa hukuncin daurin shekara Daya Babu zabin biyan tara da kuma Bulala 20.