Kotu Ta Yanke Wa Barawon Wayoyin Iphone Hukunci.

Spread the love

Wata kotun majistiri dake zaman ta dake zaman ta a jahar Kaduna ta yanke hukuncin daurin makonni 16, ga mutum mai suna Rabi’u Yusuf, bisa samun sa da laifin satar wayoyi guda 2 kirar Iphone , wadanda kudinsu ya kai naira dubu dari shida da saba’in da takwas ( N678,000).

Mai gabatar da kara Inspecter Chidi Leo, ya shaida wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin a ranar 13 ga watan satumba 2024, a Kurmin Mashi Kaduna, a shagon wata mai suna Zainab Salisu, inda ya amsa laifin da ake tuhumarsa.

Alkalin kotun mai shari’a , Ibrahim Emmanuel, ya gargadi wanda aka samu da laifin da ya kaucewa aikata dukkan wani laifi anan gaba, domin zai fuskanci hukunci mai tsanani, inda ya yanke hukuncin daurin makonni 16 a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *