Rundunar yan sandan jahar Kano, ta gurfanar da wani matshi mai suna Abdulaziz Abubakar, a gaban kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Unguwar Danbare Kano, bisa zargin sa da aikata laifin sata.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa, mutanen Unguwar ne suka yi, korafinsa a Ofishin yan sandan Dorayi Babba, da cewar matashin ya addabe su da sata cikin dare.
Mazauna Unguwar Danbaren, sun zargi .Abduaziz Abubakar, da kwarewa wajen cire Kwanukan rufin al’umma kafin ya samu damar shiga gidajensu don aikata sata.
Mai gabatar da kara Inspecter Bashir Wada, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, ta shiga ta laifi, Mugunta da kuma aikata sata.
Bayan karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masq, inda nan ta ke ya amsa laifukan.
Haka zalika an samu kwanon Rufin gidajen a wajensa, inda al’ummar Unguwar suka cika harabar kotun don gane wa idonsu.
Asibitin Unguwar Darma Zai Kara Samun Kayan Aiki Daga Kungiyar Darma Zumunta
Alkalin kotun mai Shari’a Mallam Munzali Idris Gwadabe, ya samu matashin da aikata laifin, inda ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya ba tare da zabin biyan tara ba.
Shugaban kwamitin tsaron yankin Mika’il Warure, a madadin al’ummar Danbare ya bayyana gamsuwar sa da hukuncin da kotun ta yanke masa.