Kotu ta yanke wa mai damfarar yan POS da yankakkun takaddu a matsayin kudi hukunci a Kano.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama Kano , ta yankewa, wani matashi mai suna Basiru Yusufi ( Kafinta), mazaunin garin Aujarawa a karamar hukumar Gezawa, hukuncin daurin shekaru biyu da rabi , bayan samunsa da aikata laifin zamba cikin aminci da kuma cin amana, wanda yin hakan ya saba wa sashi na 203 da 206.

Tunda fari dai ana zargin sa da zuwa wajen wani mai sana’ar POS, da wasu takaddu da ya yanka a matsayin kudi sannan ya sanya su a cikin baƙar Leda, ya kai masa domin ya yi masa Transfer har ta naira dubu dari biyar.

Sai dai mai POS din, ya duba cikin asusun su , inda ya ga saura naira dubu dari da hamsin kacal, inda dan damfarar ya ce ya tura masa naira dubu dari da hamsin din, bayan ya tura masa sai ya dauko takaddun da ya daddaure su a Kyauro, a baƙar Leda kamar kudi , sannan ya ce masa ga naira dubu dari biyar nan don haka Yaron shagon ya ajiye kudin zaije ya karo wasu a hada a tura masa.

Koda ya ji naira dubu dari da hamsin din sun shiga asusin sa na Opay, sai ya sulale yabar yaron da tarin takaddu.

Koda mai shogon ya zo , ya bayyana masa , sai suka shigar da korafinsu a sashin gudanar da binciken laifuka dake rundunar yan sandan Kano, suka bazama neman sa ta hanyar yin Tracking din asusun bankin sa na Opay.

Wata kungiya ta kalubalanci masu son a rushe masarautun Kano

Ba mu muka hana Hafsat Chuchu kin yin Magana agaban kotu ba: Barista Haruna Magashi

Bayan kama shi ne, jami’an yan sandan suka gurfanar da shi , agaban kotun, inda mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala , ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, ya amsa laifin nan ta ke.

Inda ya ce tabbas shi ne ya shirya takaddun a Leda kuma ya zambaci mai POS din da cin amanar sa.

Mai gabatar da karar ya yi roko karkashin sashi na 350, ta yanke masa hukunci bisa ikirarin bakin sa , kuma kotun ta amince da rokon.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa daurin shekaru biyu a laifin farko a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya, ko zabin biyan tarar naira dubu sittin.

A laifi na biyu kotun ta yanke masa, hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar naira dubu goma, sannan kotun ta yi umarnin ya biya mai karar kudinsa dubu dari da hamsin da kuma kudin da mai karar ya kashe wajen wahalhalun shari’a har naira dubu hamsin da biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *