Kotu ta yanke wa masu garkuwa hukuncin kisa ta hanyar rataya

Spread the love

Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Osun ta yanke wa wasu masu garkuwa biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin sace wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Adamu, tare da kashe shi.

An gurfanar da mutanen biyar a gaban alƙali bisa tuhume-tuhume da suka ƙunshi haɗa baki don yin garkuwa da mutumin da kuma laifin kisan kai, zargin da suka musanta a lokacin da aka fara gurfanar da su ranar 28 ga watan Oktoban 2021.

A lokacin zaman sauraron shari’ar, lauyan gwamnati, Faremi Moses, ya gabatar da hujjoji da ke nuna cewa mutanen biyar sun yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Adamu a ranar 17 ga watan Afrilun 2018 daga gidansa da ke ƙaramar hukumar Ede da arewa a jihar Ogun.

Lauyan ya ce mutanen sun kashe Alhaji Ibrahim Adamu bayan da iyalansa suka biya kudin fansa na naira miliyan uku.

A nasa ɓangare lauyan waɗanda ake zargin ya ce hujojjojin masu gabatar da ƙara ba su da ƙarfin da za su iya gamsar da kotu.

To sai dai a lokacin da take yanke hukunci, Mai shari’a, Kudirat Akano ta ce kotu ta samu mutanen biyar da laifuka huɗu da aka tuhume da su, inda ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *