Kotu Ta Yanke Wa Matasan Da Suka Saci Kayan Jami’ar Bayero Kano Hukunci.

Spread the love

 

Kotun Shari’ar addinin musulinci Mai namba 2 , dake zaman ta a Kofar kudu gidan Sarki Kano, ta yanke wa wasu matasa 5 hukunci bayan ta same su da aikata laifuka.

Mai gabatar da kara na Kotun ya karanto kunshin tuhume-tuhume, hada Kai, aikata laifi, shiga B.U.K da yin barna da kuma sata da muggan makamai , karkashin sashi na 120, 215, 363, 133 da 264 na Shari’ar Penel Code 2,000, nan ta ke suna amsa.

Tun a ranar 31 ga watan Augusta 2024, matasan da suka hada da, Ahmed Adam, Abdullahi Ibrahim, Aliyu Ibrahim, Ibrahim Sulaiman da Abubakar Ibrahim, suka shiga jami’ar Bayero Kano, Inda suka sace Na’urar sanyaa daki guda 20 wato AC da kuma Penel Solar 10, suka siyarwa da Abubakar Ibrahim Amma an samu wasu daga cikin kayayyakin.

Mai gabatar da karar ya roki Kotun ta yanke mu su hukuncin na nan ta ke, kuma kotun ta karbi rokon kamar yadda idongaeing, ta ruwaito.

Alkalin kotun Mai shari’a, Malam Isah Rabi’u Gaya, ya yanke mu su hukuncin daurin watanni shida-shida a laifin farko ko biyan tarar naira Dubu 10 , sai laifi na biyu kuma daurin watanni shida-shida ko biyan tarar Dubu 10.

A laifi na Uku an yanke mu su hukuncin daurin shekara Daya ko biyan tarar naira Dubu 20 , laifi na hudu daurin shekara Daya ko tarar naira Dubu 20 sai laifi na 5 kuma an Yi mu su sassauci sakamakon zaman gidan gyaran hali da tarbiya da suka da suka yi, Inda kotun taja kunnensu da su zama mutanen kirki.

Haka zalika kotun Umarce su, da su biya kudin rankon kudin satar kayayyakin naira Dubu dari 181 kowannensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *