Kotu Ta Yanke Wa Matashi Hukunci Bayan Ta Same Shi Da Laifi A Kano

Spread the love

Wata kotun shari’ar addinin musulinci da ke zaman ta, a unguwar Danbare Kano ta yanke wa  wani matashi hukuncin daurin watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba, sakamakon  samun sa da aikata laifin shiga waje ba da izini ba ,  da kuma  aikata sata.

Mai gabatar da kara Inspecter Bashir Wada, ya karan to  kunshin tuhumar da ake yi wa matashin , mai suna Abba Dahiru,  inda nan ta ke ya amsa laifin.

Tunda fari ana zarginsa da satar Somo mallakar Mohd Mustapha, mai kimar kudi naira dubu dari da sha biyar, da kuma na Haruna Tsoho mai kimar kudi naira dubu dari, amma shi anga nasa.

Haka zalika ana zargin ya kwashe wa Bashir Mustapha, wasu Karafa da kayan gyaran wutar lantarki.

Da yake yanke hukuncin mai shari’a Munzali Idris Gwadabe, ya ce matashin zai biya kudin rankon kudin kayan , tare da aike wa da shi zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya tsawon watanni shida babu zabin biyan tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *