Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Gama Kano, ta yanke wa wani matashi mai suna Imrana Ibrahim, hukuncin daurin watanni uku a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, sakamakon samun sa da aikata laifin fashin waya da wata sharbebiyar wuka.
Tunda fari dai ana zargin matashin da farwa wata Daliba da sharbebiyar wuka, inda ya kwace wayar ta da kuma Jakarta a yankin unguguwar Burgate Kano.
Bayan faruwar lamarin ne, matasan yankin suka samu nasarar kama shi tare da mika shi, hannun jami’an yan sandan jhar Kano, wadanda suka gurfanar da shi a gaban kotu.
Hisbah ta kwace kwalaban giya, ta kama mata masu zaman kansu a Kano
Tsohon gwamnan jihar Kaduna Ramalan Yero ya koma APC
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa , inda nan ta ke ya amsa laifin sa.
Alkalin kotun mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni uku a gidan ajiya da gyran hali da tarbiya ba tare da zabin biyan tara ba.