Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Gama PRP Kano, ta yanke wa Murtala Adamu hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar naira dubu talatin ( 30.000).
Ana zargin Murtala da aikata laifukan tayar da haniya da aikata badala wanda yin hakan ya saba da sashi na 275 na kundin SPCL.
Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda nan ta ke ya amsa laifinsa.
Haka zalika mai gabatar da karar ya roki kotun ta yanke masa hukunci sakamakon ya amsa laifinsa kuma kotun ta amsa rokon na sa.
karanta wannan labarin Ana neman wadanda suka fitar da dala miliyan shida da sa-hannun bogi na Buhari
Tunda fari dai an kama Murtala Adamu tare da Murja Ibrahim Kunya, a unguwar Hotoro, lokacin da jami’an hukumar Hisbah na jahar Kano, sukaje yankin bayan samun korafin al’ummar unguwar.
Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar naira dubu talatin.
Sannan kuma kotun ta raba alakar su da Murja Kunya bashi ba ita, sannan kar ya sake zuwa Unguwar tsawon shekaru biyu, idan kuma aka ganshi za a sanar wa da kotun an kuma bashi form ya cike tare da sanya hannu.