Kotu Ta Yanke Wa Mutumin Da Ya Haura Gida Ya Saci Dubban Dalolin Amurika Hukunci A Kano.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Unguwar Gama Kano, ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin shekaru uku da rabi, sakamakon samun sa da aikata laifin satar Dalar Amurika dubu saba’in da hudu, kwatankwacin naira miliyan hamsin da tara Kafin farashin Dalar ya tashi.

Jaridar idongari.ng, ta ruwaito cewa, a shekarar 2023, Wanda ake tuhuma, Jibrin Dauda, Mazaunin Kofar Fada, karamar hukumar Bagwai Kano, ya haura gidan wani mai suna Hon. Alhaji Zakari Ibrahim , inda ya yi masa awon gaba da Dalar Amurika Dubu Saba’in da hudu kwatankwacin naira miliyan hamsin da Tara tun a wancan lokacin.

Ana tuhumar sa da laifin shiga ta laifi, haura gida da kuma yin sata, Wanda yin hakan ya Saba wa sashi na 212, 133, 216 na kundin SPCL.

Mai gabatar da Kara, Aliyu Abidin Murtala, ya karanto ma sa kunshin tuhumar da ake yi masa, inda nan ta ke ya amsa laifinsa.

Mai gabatar da karar ya yi roko karkashin sashi na 356 karamin kashi na 2, don kotun ta yanke wa, wanda ake tuhumar hukunci sakamakon amsa laifin sa da ya yi , kuma kotun ta amsa rakon.

Mai Shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukunci , a laifin farko daurin shekara daya ba tare da zabin biyan Tara ba, laifi na biyu kotu ta daure shi daurin shekaru biyu da rabi , ba tare da zabin biyan Tara ba.

Tun a baya ya chanja kudin zuwa naira a kasuwar WAPA Kano, har ya siyi Motoci da shugunan da ya bude harda Mota kirar Akori Kura da shagunan sayar da mai.

An dai samu kayayyaki Masu kimar kudi naira miliyan talatin da dubu dari bakwai a hannunsa.

Sannan kuma kotun ta umarci Wanda aka yanke wa hukuncin , ya biya sauran kudin da aka rasa, naira miliyan 28 da dubu 760 da naira 400, kamar yadda jaridar idongari. ng, ta ruwaito.

Haka zalika zai biya mai Karar kudaden da ya kashe da bata masa lokaci, kimanin naira dubu Dari biyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *