Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a Gama PRP Kano, ta yanke wa wani mutum mai suna Haruna Isiyaka Gyadigyadi, hukunci daurin watanni 9 a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya, sakamakon Samun sa da aikata laifin sata.
Mai gabatar da Kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar sa ake yi masa , ta shiga ta laifi da kuma aikata sata , Wanda yin hakan ya Saba da sashi na 212 da 133 na kundin Penel Code.
Tun Ranar 2 ga watan Mayu 2024, ake zargin Mutumin da haura wa gidan Ghali Musa Rogo Mazaunin Unguwar Na’ibawa a Karamar hukumar Kumbotso, inda ya sace masa wayoyin salula guda biyu da kuma Power Bank 1 , Masu kimar kudi naira dubu dari da talatin (130,000).
Bayan karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa nan ta ke ya amsa laifin baaa tare da ya bata wa kansa ba.
Mai gabatar da karar ya roki kotun ta yanke masa hukuncin nan ta ke sakamakon amsa laifin sa da ya yi.
- Kungiyar Likitoci Ta Fusata Kan Dakatar Da Likita A Kano
- Kungiyar Likitoci Ta Fusata Kan Dakatar Da Likita A Kano
Mai Shari’a Malam Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukunci daurin watanni shida, a laifin shiga ta laifi ba tare da zabin biyan Tara ba, a laifi na biyu daurin watanni uku, ko zabin biyan tarar naira dubu Goma (10,000).
A karshe kotun ta yi umarnin a Mayar wa da mai kayan wayoyinsa.