Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin daurin watanni 9 bisa samunsa da laifin satar babur a ma’aikatar gwamnatin Kano.

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta, a unguwar Gama PRP Kano, ta yanke wa wani Mutum hukuncin daurin watanni tara a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya ,sakamakon samun sa da kotun ta yi dumu-dumu da aikata laifin satar Babur.

Mutumin ya shiga ma’aikatar kasa ta jahar Kano ( Land and Survey) , inda ya sace wani Babur kirar Jojo mai launin Ja, mai kimar kudi naira dubu dari uku da hamsin mallakar wani brahim Mansur.

An tuhimi mutumin mai suna Bashir Sani Ungoggo, da laifin shiga ta laifi da aikata sata, wanda ya saba da sashi na 216 da 133 na kundin SPCL.

Mai gabatar da kara Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa , inda nan ta ke ya amsa laifin, sai dai mai gabatar da karar ya shaida wa kotun cewar ya saba aikata laifin.

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmed, ya amince da rokon , inda ya yanke masa hukuncin daurin watanni 9, a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya , kuma ya umarci a ba wa mai baurdin kayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *