Kotu Ta Yankewa Mai Satar Kayan Masallacin Juma’a Hukunci A Kano

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a Unguwar Gama PRP Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin daure shekara daya da Rabi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya , sakamakon samun sa da aikata laifin sata a masallacin juma’a.

Tunda fari yan I am it if Masallacin Juma’a na garin Gayawa ne , suka cafke matashin mai suna Yusuf Abdurraham Gayawa, bayan ya yi awon gaba da Baturan Sola guda 2 da kuka Amplifier ta Lasifikar masallacin Masu kimar kudi naira dubu dari da tamanin.

Laifukan da ake zargin matashin da aikata wa , sun Saba wa sashi na 212 da 133 na kundin SPCL.

Mai gabatar da Kara, Aliyu Abidin Murtala, ya karanto masa kunshin tuhumar da ake Yi masa, inda nan ta ke ya amsa.

Mai Shari’a Mallama Nura Yusuf Ahmed, ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida a laifin farko ba tare da zabin biyan Tara ba.

Haka zalika an yanke masa hukuncin daurin shekara daya a laifi na biyu ko kuma zabin biyan Tara naira dubu 40.

Alkalin kotun yaja kunnensa ya zama mutumin Kirki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *