Kotu Ta Yankewa Ummin Mama Hukunci Saboda Yada Badala A Tiktok

Spread the love

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zamanta, a hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta yankewa Rukayya Ibrahim wadda akafi sani da Ummin Mama, hukuncin daurin watanni bakwai a gidan a jiya da gyaran hali da tarbiya ko zabin biyan tarar naira dubu hamsin, saboda da samun ta da laifin yada tsiraicinta a shafin Tiktok da tayar da tarzoma da kuma lalata tarbiya a kafofin sada zuminta.

 

Tunda farko mun ruwaito muku cewa hukumar hisbah ta jihar Kano ce ta kama Ummin Mama, a cikin gidan namun daji dake Zoo road, daga bisani kuma hukumar, ta miƙa ta ga ƴan sanda su kuma suka cike mata takardun tuhuma tare da gurfanar.

Matashiyar Ruƙayya Ibrahim, ta ce da zarar ta fito daga gidan yarin wa’azi za ta koma yi a shafukan sada zumunta sanye da Hijabi, duba da wahalar da ta sha a gidan yarin.

Idan ba a manta ba  Wani mutum ya Yi wa alkalin dake Sauraren shari’ar ta yin bashi Dalolin Amurika don ya saki yar TikTok din, amma alkalin kotun Sani Tamim Hausawa yayi fatali da tayin cin hancin .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *