Kotun shari’ar addinin muslinci ta Gama PRP Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, ta yi umarnin a binciki lafiyar kwakwalwar yar din nan Murja Ibrahim kunya.
Yar Tiktok: An Yanke Wa Ramlat Princess Hukuncin Zaman Gidan Yari na watanni 7
Ana azumi kan tsadar rayuwa a jihar Borno
Cikin wani kwaryar kwaryar hukunci da kotun ta yi ta ayyana cewar a ajiye Maurja a karkashin kulawar likita kuma hukumar Hisba ta dinga lura da ita.
Mai shari’a Nura Yusuf ya bayyana cewar kasancewar ita murja ta nuna wani hali wanda yake nuna cewar ko dai tana cikin maye ko kuma kwakwalwarta bata da lafiya, a dan haka ne kotun ta yi umarnin ma’aikatar lafiya ta binkici kwakwalwar ta.
An kuma ayyana cewar zata kwashe watanni uku a karkashin kulawar likitoci da hukumar Hisba.
A karshe kotun ta yi addu’ar Allah ya shirya mana zuri’a.
DALA FM