Kotu ta yi watsi da buƙatar cire ajami a kuɗin Najeriya

Spread the love

Wata babbar kotun tarayya a Legas kudancin Najeriya ta yi watsi da wata ƙara da aka shigar gabanta na neman cire rubutun ajami a kuɗin ƙasar.

Barista Malcolm Omirhobo ne ya shigar, inda yake kalubalantar Babban Bankin Najeriya CBN kan kotu ta umarce shi domin cire rubutun ajami na haruffan larabci daga takardar kuɗin ƙasar.

Kotun ta yi watsi da karar a ranar Talata inda mai shari’a Yellim Bogoro ya nuna cewa wanda ya shigar da karar ya gaza bayar da hujjoji da za su nuna cewa Babban Bankin Najeriya ya Sanya rubutun ajami da wata mummunar manufa.

Kafin zartar da hukuncin, kotun ta ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci inda ya jaddada da cewa babu fifita wani addini ko kabila.

Mai shari’a Yellim, wanda ya yi watsi da karar ya kara da cewa kotun ta dogara ne da shari’ar Cif Gani Fawehinmi da Akilu da aka yi a shekara ta (1998), inda kotun ta ce yayin da Cif Omirhobo ke da gurbi don sauraron kararsa amma kuma ya kasa bayar da isasshiyar hujja da za ta nuna cewa tsarin da Babban Bankin Najeriya ya yi don ci gaba da amfani da rubutun Ajami kan takardun kudin Naira da rubutun Larabci, an yi shi ne da muguwar manufa.

Sauran wadanda suke cikin shari’ar sun hada da kungiyar kare haƙƙin Musulmi karkashin daraktanta Farfesa Ishaq Akintola da kuma Umar Kalgo, wani fitaccen lauya mazaunin jihar Kebbi.

Babban Daraktan kungiyar kare hakkin Musulmi , Farfesa Ishaq Akintola, bayan yanke hukuncin ya ce wannan nasara ce mai cike da albishir ga Musulmi da masoya Musulunci a fadin kasar.

A martanin da ya mayar kan hukuncin, Mista Omirhobo ya ce ya nemi a ba shi kwafin hukuncin kuma zai yi nazari don daukar mataki na gaba.

Da yawa dai ba su fahimci cewa kafin zuwan turawan mulkin mallaka galibin ana amfani ne da haruffan larabci domin rubuta harsunan Afirka da ake kira “Ajami.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *