Kotun ƙoli ta tabbatar da hukuncin daurin shekara 5 kan Farouk Lawan

Spread the love

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin shekara biyar da aka yankewa tsohon dan majalisar wakilai Farouk Lawan bisa samunsa da laifin karbar cin hancin dala 500,000 daga hannun dan kasuwa Femi Otedola, shugaban kamfanin Zenon Petroleum and Gas Limited

Ɗaukaka karar ya buƙaci a soke hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari tare da sake shi a kan tuhume-tuhume biyu daga cikin ukun da ake tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa da gwamnatin tarayya ta yi masa.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

A hukuncin da mai shari’a John Okoro ya shirya amma mai shari’a Tijjani Abubakar ya karanta, kotun kolin ta ce ƙarar da Lawan ya shigar ba ta da wani dalili kuma ta yi watsi da shi.

Kwamitin alƙalain mutum 5 a wani mataki na bai ɗaya sun tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a shekarar 2022 wanda ya tabbatar da hukuncin da aka yankewa Lawan na shekaru biyar dangane da tuhume-tuhume uku da ake tuhumarsa da shi.

Kotu ta yanke wa matashin da ta samu da laifin fashin wayar daliba hukunci a Kano

Hukuncin kotu: Yan Kasuwar Magani ta Sabongari a Kano sun rufe shagunansu bayan sun yi sallar Alkunut .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *