Kotun ɗaukaka ƙara ta jaddada dakatar da kasafin kuɗin da Gwamnan Rivers Fubara ya yi

Spread the love

Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta tabbatar da hukuncin kotun tarayya da ya ba da umarnin dakatar da kasafin kuɗin da Majalisar Dokokin jihar Rivers ta amince da shi ƙarƙashin jagorancin Edison Ehie.

Kotun ta kori ƙarar ce wadda Gwamna Siminalayi Fubara ya ɗaukaka bayan ‘yanmajalisar jihar biyar da ke biyayya gare shi sun amince da shi kasafin na naira biliyan 800.

Kotun ta ce ta kori ƙarar ne saboda rashin cancanta.

Ta ƙara da cewa gwamnan ya janye bayanan da ya gabatar wa kotun ƙasa game da lamarin, a saboda haka ba zai yiwu ya ɗaukaka ƙara ba kan batun da bai ƙalubalance shi ba tun da farko.

Rikici tsaknin Gwamna Fubara da tsohon maigidansa kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, na ci gaba da ruruwa, inda a makon da ya gabata ma gwamnan ya rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi da ke yi masa biyayya bayan sun ci zaɓe a jam’iyyar APP.

Hakan ta faru ne bayan sun fice daga jam’iyyarsu ta PDP mai mulkin jihar, yayin da ake kokawar gwada iko tsakaninsa da Wike, wanda Fubara ya gada a mulkin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *