Kotun ƙoli ta tabbatar da zaɓen gwamna Peter Mbah na Enugu

Spread the love

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da zaɓen da aka yi wa Peter Mbah na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Enugu a zaɓen gwamnan jihar na watan Maris.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a zaman da ta yi yau Juma’a.

A lokacin zaman nata, ɗaukacin alƙalai biyar na kotun sun yi watsi da ƙarar da jam’iyyar LP da ɗan takararta na gwamnan jihar, Chijioke Edeoga suka ɗaukaka suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen na ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta bayyana cewa babu wata hujja ƙwaƙƙwara da aka gabatar wadda zai sanya ta ta soke hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara da kuma na kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar ta Enugu, waɗanda dukkanin su suka tabbatar da nasarar ta Mbah.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

An karrama yan sanda huɗu saboda ƙin karɓar cin hancin miliyan 8.5 a Taraba

Sakamakon zaɓen gwamnan na jihar Enugu da Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta fitar dai ya nuna cewa Peter Mbah shi ne ya lashe zaɓen da ƙuri’u 160,895.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *