Kotun Ƙolin Najeriya ta ce gwamnoni su daina riƙe kuɗin ƙananan hukumomi

Spread the love

Kotun Ƙolin Najeriya ta ce riƙe kuɗin ƙananan hukumomi da gwamnaonin jihohin ƙasar ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Cikin hukuncin da ta yanke kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce kotun ta fahimci cewa gwamnatocin jihohin ƙasar sun shafe fiye da shekara 20 ba tare da sakar wa ƙananan hukumomin mara ta fuskar kuɗaɗensu ba.

Alƙalin kotun ya ci gaba da cewa tun tsawon wanan lokaci, ƙananan hukumomin ba sa samun kuɗaɗen da ya kamata su samu daga gwamnonin jihohin ba, waɗanda ke kashe kuɗin ta hanyar yin ayyuka a madadin ƙananan hukukomin.

Mai shari’a Agim ya ce dole ne ƙananan hukumomin ƙasar 774 su riƙa amfani da kuɗaɗensu da kansu ba tare da sa katsalandan daga gwamnonin jihohi ba.

Haka kuma alƙalin ya yi watsin da ƙorafin da gwamnonin suka yi ta bakin lauyoyinsu.

Gwamnatin tarayyar ta kuma buƙaci kotun ta dakatar da gwamnonin jihohin ƙasar, daga rushe zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *