Kotun Daukaka Kara: Sheik Abduljabbar Kabara Ya Datakatar Da Lauyan Da Yake Kare Shi.

Spread the love

Babbar kotun jaha ɓangaren ɗaukaka ƙara ta ɗage sauraron ɗaukaka ƙarar da malam Abduljabbar Sheikh Nasir Kabara ya yi a gabanta.

Hakan ya biyo bayan wata takarda da Abduljabbar ɗin ya aikewa kotun wadda ya sanarwa da kotun cewar ya janye lauyansa daga cikin shari’ar.

Kotun ta ɗage shari’ar har zuwa lokacin da malamin zai gabatar da wani lauyan a gaban ta.

Malam Abduljabbra dai ya ɗaukaka karar ne akan hukuncin kisan da kotun shari’ar muslunci ta kofar kudu ta yanke masa a baya bisa samun sa da laifi.

Babbar kotun shari’ar Muslunci ta kofar kudu ta yankewa Abduljabbar hukunci kisa ta hanyar rataya sakamakon kama shi da laifin batanci, sai dai kasancewar malamin bai yadda da hukuncin ba hakan yasa ya ɗaukaka ƙararar.

Yayin zaman Kotun na yau Laraba 15-05-2024 karkashin jagorancin Mai Shari’a Nasir Saminu, an gabatar da takardar dakatar da lauyan wadda Malamin ya sanya wa hannu a ranar 10-05-2024.

Sai dai lauyoyin Gwamnati sun nemi kotu ta kori neman, da bukatar gyara a kan bayanan da Kotun baya ta yi amfani da su wajen yanke masa hukuncin kisa.

Sai dai kuma kotun ba ta karbi rokon lauyoyin Gwamnatin ba.

Dala fm.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *