Alƙalan kotun hukunta manyan laifuka wato ICC sun bayar da sammacin kama firaministan Isra’ila da tsohon ministan tsaron ƙasar da wasu kwamandojin Hamas.
A wata sanarwa da ta fitar, ta bayyana cewa kotun ta yi watsi da yunƙurin Isra’ila na ƙalubalantar ikon da kotun ke da shi kan sauraron shari’ar, inda ta saurara ƙarar tare da bayar da sammacin kama Netanyahun da Yoav Gallant.
Haka kuma an bayar da sammacin kama Mohammed Deif, duk da cewa sojojin Isra’ila sun ce sun kashe shi a wani hari a Gaza a watan Yuli.
Alƙalan sun ce sun gamsu da hujjojin cewa mutanen uku sun “aikata laifukan yaƙi” da wasu laifukan cin zarafin mutane a yaƙin Isra’ila da Hamas. Sai dai Isra’ila da Hamas ɗin duk su musanta aikata laifukan yaƙi.
Yanzu hankali ya koma kan ƙasashe mambobin kotun duniyar guda 124 domin yanke shawarar tabbatar da umarnin kotun ko su yi watsi da shi.
A watan Mayu ne mai gabatar da ƙara na kotun hukunta manyan laifuka, Karim Khan ya buƙaci kotun ta bayar da sammacin kama Netanyahu da Gallant da Deif da wasu kwamandojin Hamas biyu, waɗanda an riga an kashe su wato Ismail Haniyeh da Yahya Sinwar. Duk da cewa Isra’ila ta ce ta kashe Deif, kotun ta ce ba ta tabbatar da hakan ba.
Mai gabatar da ƙarar ya shigar da ƙarar ce saboda abin da ya biyo bayan harin Hamas na 7 ga Oktoban 2023, wanda ya yi sanadiyar kashe kusan mutum 1,200 a arewacin Gaza, sannan suka yi garkuwa da mutum 251.
Isra’ila ta ƙaddamar da mayar da martani, inda ta kashe aƙalla mutum 44,000 a Gaza, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta yankin wanda ke ƙarƙashin Hamas ta bayyana.
An zargi jagororin Hamas da kisa da garkuwa da mutane da fyaɗe da azabtarwa.
A gefe guda kuma an zargi Isra’ila da kai hare-hare kan fararen hula da gangan da amfani yunwa a matsayin makamin yaƙi da kashe-kashe