Kotun Kano za ta ci gaba da shari’ar Ganduje

Spread the love

Wata babbar kotu a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa za ta ci gaba da sauraren shari’ar zargin almundahanar da ake yi wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Hafsat da wasu mutum shida duk da kasancewar ba su bayyana a kotun ba.

Gwamnatin Kano ce ta shigar da karar tsohon gwamnan jihar inda take zarginsa da abubuwa da dama ciki har da cin hanci da rashawa, sai dai tun watan Mayun nan da aka shigar da karar mutum guda ne kadai cikin wadanda ake karar ya bayyana a kotun.

Lauyan gwamnatin Kano, Adeola Adedife, ya gabatar da bukatu uku a gaban kotun, kasancewar wadanda ake karar ba su bayyana kotu ba.

Bukatar farko da Adeola ya nema ita ce, kotu ta bayar da odar a kamo wadanda ake karar a kawo su gaban kotun tun da an wallafa takardar sammaci a jaridu kuma ba su bayyana a kotu ba.

Ya kuma nemi a basu rana su fara gabatar da shaidu.

Sai dai lauyan kamfanin Lamash Properties Limited Nuraini Jimoh ya soki wadannan bukatu, inda ya shaida wa kotun a madadin sauran wadanda ake karar cewa ai ba a basu takardar sammaci ba, sannan kuma ya soki takardar sammacin da aka baiwa kamfanin da ya wakilta.

Ya shaidawa kotun cewa sun shigar da sukar cewa kotun bata da hurumin sauraron shari’ar inda ya nemi a fara sauraron bukatunkafin a saurari komai a zama na gaba.

Sannan ya nemi kotun ta yi watsi da bukatun masu kara yana mai cewa za a fara sauraron gundarin shari’ar amma a cewarsa masu kara ba su nuna cewa a shirye suke ba.

Daga nan ne kuma mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dage zaman tare da cewa sai karfe biyu za ta yi kwarya-kwaryar hukunci a kan bukatun da banagrorin suka gabatar, sannan kuma ta bayar da umarnin cewa kada lauyoyi su yi magana da ‘yan jarida.

Bayan mai shari’a ta dawo ne sai ta yi hukuncin cewa ta amince da bukatar masu kara na ci gaba da shari’ar tare da ayyana cewa tamkar an karantawa wadanda ake karar tuhume-tuhume ba su amince ba tare da fara gabatar da shaidu.

Sai dai mai shari’ar bata amince da rokon a kamo wadanda ake karar ba. Sannan kuma kotun tace Nuraini Jimoh ba shi da hurumin yin magana a madadin wadanda basu bayyana a kotun ba tun da yana wakiltar wanda ake kara ne wato na shida kadai.

Sai dai mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta amince da bukatar da Nuraini Jimoh ya nemi na fara sauraron sukar da ya yi cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar kafin kotu ta saurari komai tukuna.

Mai shari’a Amina Adamu Aliyu ta dage zaman kotun zuwa 23 da 24 ga watan Oktoban shekarar nan don fara sauraron gundarin shari’ar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *