Hukuncin Kotun Koli: Gamayyar hukumomin tsaro sun bada tabbacin samar da ingantaccen tasaro a Kano

Spread the love

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya jagorancin wani muhimmin taro, tare da gamayyar hukumomin tsaron jahar , don bada ingantaccen tsaro gabanin hukuncin da kotun Kolin Nigeria zata yanke har zuwa bayan hukuncin zaben gwamnan Kano.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullah Haruna Kiyawa, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a daren ranar Alhamis.

Yansanda sun kama ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga.

Ya kara da cewa ,daman an saba gudanar irin wannan ganawar amma wannan an yi ta ne kan shirin  bayar da cikakken tsaro dan kare rayukan al’uma da dukiyoyin su har zuwa bayan kotun koli zata yi hukuncin ta a zaben gwamnan jahar.

Sanarwar ta kara da cewa gamayyar hukumomin tsaron sun tattaunawa muhimman batutuwa da suka shafi tsaro, dan magance dukkanin wata barazana da zata biyo bayan hukuncin kotun kolin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *