Kotun Koli ta hana gwamnonin Najeriya rusa shugabannin ƙananan hukumomi

Spread the love

Kotun Ƙolin Najeriya ta haramta wa gwamnonin jihohin ƙasar rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar.

A hukuncin da ta yanke ranar Alhamis kotun ta ce rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar.

Ministan shari’ar ƙasar ne ya shigar da ƙara a gaban kotun a madadin gwamnatin tarayya, inda ya buƙaci kotun ta hana gwamnonin jihohin rusa zaɓaɓɓun shugabannin ƙanann hukumomin.

Tun da farko, gwamnonin jihohin ƙasar 36, sun nuna adawa da ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *