Kotun Koli ta tabbatar da Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP a matsayin zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Adamawa.
A safiyar Laraba ne Mai Shari’a John okoro ya karanta hukuncin Kotun, wanda ya watsi da ƙarar ’yar takarar Jami’yyar APC, Aisha Dahiru Binani da ke ƙalubalantar nasarar Fintiri.
Kwamitin alkalai biyar na kotun d yake jagoranta ya bayyana cewa Kwamishinan Zaben INEC na jihar, Hudu Ari, ya aikata laifi wajen hana baturen zaben bayyana sakamakon zaben kamar yadda dokar zabe ta tabbatar.
Mai Shari’a John Okoro ya ce rashin barin baturen zaben ya bayyana sakamakon zaben, ya haifar da ruɗani.
Ya ce dokar zabe ta bayyana karara baturen zabe ne kaɗai yake da hakkin na sanar da sakamakon zabe.
Idan za a iya tunawa, a yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zabe ne Hudu Ari ya sanar da cewa A’isha Binani ta lashe zaben.
Tun a lokacin INEC ta kira Hudu Ari domin ya amsa tambayoyi kan abin da ya aikata, kuma a halin yanzu yana ci gaba da fuskantar shari’a.