Kotun Najeriya ta hana belin jami’in Binance

Spread the love

Wata babbar kotun tarayya a Abuja babban birnin Najeriya ta yi watsi da buƙatar bayar da belin jami’in kamfanin kuɗin kirifto na Binance, Tigran Gambaryan wanda ya shafe fiye da kwana 40 a tsare a gidan yarin Kuje da birnin tarayyar.

Yayin da yake gabatar da hukuncin, mai shari’a Emeka Nwite ya ce ya yi nazarin takardar neman belin da aka gabatar masa, sai dai ya ce akwai yiwar mista Gambaryan zai iya tserewa idan aka bayar da belinsa.

Hukumar EFCC ce gurfanar da jami’in tare da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla, da kuma kamfanin Binance a gaban kotun bisa zarge-zarge biyar masu alaƙa da almundahanar kuɗi da ya kai kimanin dala miliyan 35.4 a shafin kamfanin.

Hama ma hukumar tara haraji ta ƙasar, FIRS na zargin mutanen uku da laifuka hudu da suka jiɓanci ƙin biyan haraji.

Waɗanda ake zargin dai sun musanta duka zarge-zargen.

An dai fara shari’ar ta yau ne kan almundahanar kuɗi, ta hanayr gabatar da shaida daga hukumar kula da hannayen jari ta ƙasar.

A makon da ya gabata ne dai shugaban kamfanin na Binance, Richard Teng ya zargi wasu jami’an gwamnatin Najeriya da neman a ba su cin hancin dala miliyan 150, domin kashe maganar.

Zargin da hukumomin ƙasar suka musanta, suna masu bayyana shi da ”ɓata suna” da kuma kawar da hankalin mutane kan shari’ar da ke gudana.

Kawo yanzu dai ba a san inda Nadeem Anjarwalla yake ba bayan tserewarsa daga hannun hukumomin Najeriya.

To sai dai hukumomin ƙasar sun ce suna aiki da jami’an ‘yan sandan ƙasa da ƙasa, a wani mataki na samun sammacin ƙasa da ƙasa a ƙasa domin kama shi a duk inda yake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *