Kotun ta yanke hukunci ga wanda ya chakawa jami’in NDLEA wuka a Kano

Spread the love

Wata kotun tarayya dake zaman a Kano karkashin jagorancin mai Shari’a MN Yunusa ta yanke hukunci ga wasu mutane 22 da aka same su da laifin tu’ammali da miyagun kwayoyi, daga Cikin su kuma akwai wanda ya tsakawa jami’in hukumar NDLEA wuka.

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kano ce ta samu nasarar kama mutane 22 a cikin watan Yulin 2024 a yakin da take yi da safarar miyagun kwayoyi da kuma sha da fataucin miyagun kwayoyi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar reshen jihar kano Sadiq Muhammad Maigatari ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aikowa kadaura24 a Kano.

Ya ce daga cikin wadanda aka yankewa hukuncin har da Abubakar Muazu, wanda aka kama shi da caka wa wani jami’in NDLEA da kansa Mu’azu wuka. Jami’an sun kama Muazu Sannan suka kama yaransa da kuma kwato wasu kwayoyi da yake sayarwa .

 

Saurari karin haske daga bakin kakakin hukumar NDLEA reshen jahar Kano Sadik Muhammed Maigatari….

Bayan samun sa da laifi Kotun ta yankewa Abubakar Muazu hukuncin daurin shekaru 3 a gidan yari daga hannun . “Wannan laifin zai zama izina ga duk masu neman kawo cikas ga hukumar NDLEA wajen gudanar da muhimmin aikinta”.

Sanarwar ta ce hukumar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen cigaba da yakar masu sha da fataucin miyagun kwayoyi a jihar kano da kasa baki daya.

Yayin da yake godiya ga al’umma shugaban hukumar NDLEA, Brig. Janar Mohammed Buba Marwa, ya bukaci al’umma da su cigaba da baiwa jami’an hukumar hadin kai da goyon baya don cimma manufarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *