Kotun koli za ta sanya ranar yanke hukunci a ƙarar da jam’iyyar APC da ‘yar takarar gwamna, Aisha Dahiru, (Binani), suka shigar suna ƙalubalantar sahihancin zaɓen gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa.
Kotun sauraron ƙorafin zaɓe da kotun ɗaukaka kara sun yi watsi da ƙarar da Binani ta shigar na kalubalantar nasarar Finitiri a zaben gwamna da aka gudanar ranar18 ga watan Maris na 2023.
Likitoci sun dakatar da ayyukansu a Asibitin Murtala da ke Kano
Ana neman wata sarauniyar kyau a Najeriya kan zargin safarar kwaya
Alƙalan kotun ƙoli biyar, ƙarƙashin jagorancin John Okoro sun ɗage ci gaba da shari’ar bayan sun saurari bahasi na ɓangarorin da lamarin ya shafa a yau Litinin.
Babban abin da Binani ta ce, ta bakin lauyanta, Akin Olujimi, a zaman da aka yi na yau, shi ne cewa bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnar jihar mai cike da ce-ce-ku-ce da Kwamishinan zabe, Hudu Ari ya yi na kan ƙa’ida ne.
Har Yanzu Kuna Tare Da Mu —Martanin ECOWAS Ga Nijar, Mali Da B/Faso
Matakin na ranar Litinin ya zo ne watanni bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Adamawa tare da yin watsi da ƙarar da Binani ta shigar da cewa bai cancanta ba.