Wasu kotun tafi da gidanka a jihar Kano ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wasu mutum 632 waɗanda ake zargi da tayar da yamutsi da farfasa kaya da sata a tarzomar ta da biyo bayan zanga-zangar tsadar rayuwa.
An kafa kotunan uku wadanda kotunan majisteret ne a hedikwatar ‘yan sanda Kano saboda yawan mutanen ta yadda za a samu damar tuhumarsu.
Gwamnatin Kano ce ta gurfanar da mutanen da suka kai 632 a gaban kotunan tafi-da-gidanka uku wadanda kotunan majisteret ne, yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da bincike akan tarzomar da ta tashi lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa ranar daya ga watan da muke ciki.
Haruna Isa Dederi, kwamishinan shari’a ta jihar Kano ya ce mafi yawan wadanda aka gurfanar din ‘yan kasa da shekara ashirin ne, ciki har da ‘yan wasu jihohi.
Kotunan dai sun dage zaman sauraron wannan kara zuwa 19 ga Agusta don ci ga da shari’ar.Gwamnatin Kanon dai ta tabbatar da cewa nan gaba za ta kafa wani kwamitin bincike game da zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma da sace-sacen dukiyoyi da rasa rayuka don tabbatar da adalci.
Har yanzu babu cikakken bayani kan adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko jikkata yayin zanga-zangar, kuma a kwana na shida da fara zanga-zangar tsadar rayuwa yau a Kano masu zanga-zangar basu fito ba, amma daya daga cikin kungiyoyin sun ce suna tattaunawa ne amma basu jingine zanga-zanga ba.