Kowa ya debo da zafi: Kotu ta tsare matashin da ake zargi da fasa gilashin motar yan sanda da wayar salularsu a Kano

Spread the love

An gurfanar da wani matashi agaban kotun majistiri dake zaman ta , a unguwar Norman’sland Kano , karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Mansur Yola, bisa zarginsa da farwa motar jami’an yan sanda suka fasa mu su Gilashi da kuma wayar Salula daya, a lokacin da suke gudanar da aikin kwantar da riciki a unguwar Burget.

Matashin mai suna Mubarak Umar , ana zarginsa da wasu abokansa ciki harda wadanda suka gudu , sai kuma wasu da kotu ta aike da su zuwa gidan gyaran hali a kwanakin baya.

Ana zarginsa da laifin hada baki, mallakar muggan makamai da yin barna.

Lauyan gwamnatin jahar Kano, Barista Aminu Kawu ya roki kotun a karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa, bayan karanto masa ne ya musanta zargin.

Alkalin kotun Ibrahim Mansur Yola , ya bada umarnin tsare shi a gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya har zuwa ranar 18 ga watan Janairun 2024 don sake gabatar da shi .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *