Ku Maida Hankali Wajen Ilimin Yara Da Kula Da Tarbiyarsu Hon. Abubakar Jazuli Usman Gaya

Spread the love

Shugaban Karamar Hukumar Gaya Hon Abubakar Jazuli Usman Gaya Ya yi  Wannan Kiran ne lokacin da  Yake Karbar Shugabannin Kungiyar Malaman Makaranta Reshen Karamar Hukumar Gaya a Ofishinsa.

Hon Abubakar Jazuli Usman Gaya ya bayyana Ilimi da cewa shi ne kashin Bayan ci Gaban kowa Ce Al-uma ta Fuskar ci Gabansu,ya Kuma bada tabbacin shugabancin karamar Hukumar Na ci gaba da bada Kulawa a  harkar Ilimi Wajen Samar da Kayan Koyo da Koyarwa da Kayan Makaranta ga dalibai.

Anasa Bangaren Shugaban Kungiyar Malaman Makaranta Reshen Karamar Hukumar Gaya Kwamared Kamaludden Idris Gaya Ya Ce Sun Zo Ofishin Shugaban Karamar Hukumar ne domin taya shi Murna tare da Gabatar da Kansu gareshi dan ci Yar da Harkokin Ilimi ga a Fadin Yankin Na Gaya.

Daga nan, Ya yi Kira ga Iyayen Yara da Su dada maida hankali Wajen tura yaransu Makarantun Akan Lokaci tare da Samar Musu Da Kayan Koyo da koyo da Koyarwa.

A Jawabinsa Kansilan Ilimi na Yankin Alhaji Yusif Sarki ya bayyana farin cikinsa bisa Wannan Ziyara tare da Fatan zasu yi Aiki tukuru dan ganin an sami Nasarar Da ake Bukata.

Haka Zalika,Shugaban Karamar Hukumar Gaya ya Karbi Bakuncin Shugabannin Kungiyar Mahauta reshen Karamar Hukumar Gaya.

Wadanda suka zo Ofishin dan taya shi Murna ,tare da Gabatar da Jawabai game da Yadda za a kawowa Karamar Hukumar Gaya ci Gaba mai anfani,ta hanyar yin alkawarin Samar da managartan aikace aikacen ci Gaba mai anfani.

A Wani ci Gaban Kuma Hon Abubakar Jazuli Usman Gaya ya Jagoranci Kaddamar da rabon Kayan Koyo da Koyarwa ga ‘Ya’Yan Marayu Karkashin daga Ofishin mai Bawa Gwamna Shawara Akan Yara marayu, Wanda Shugaban Kungiyar Dalibai Na Gaya Kwamared Mustapha Muktar Dan Gishirin Gaya ya wakilceta a Wajen Kaddamar da rabon Kaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *