Ƙaramin ministan tsaro, Alhaji Bello Matawalle ya yi gargaɗi ga masu ba ƴanbindiga bayanai da su tuba, ko kuma su aika su lahira.
Matawalle ya yi wannan bayanin a ƙauyen Gundume da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sokoto a lokacin da ya kai ziyarar aikin da sojojin ke yi a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ministan ya ce, “wannan ƙauyen a da cike yake da mutane, inda ake gudanar da hada-hada sosai. Ina tabbatar muku cewa za a samu zaman lafiya. Za mu kafa sansanin soji a nan.
“Amma kuma dole ku ji tsoron Allah. Masu ba ƴanbindiga bayanai a kan jami’an tsaro da zirga-zirgar mutane su daina. Ko dai ku daina, ko mu aika ku lahira,” in ji shi.
Tun farko kuma a ranar Laraba a wajen ƙaddamar da aikin soji na “Fansan Yamma”, ministan ya yi kira da a ba jami’an tsaro haɗin kai domin samar da zaman lafiya a yankin.