Mataimakin shugaban majalissar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sanar da sauya wajen daurin auren Yarsa daga jahar Kano zuwa birnin tarayya Abuja.
Hakan dai na zuwa ne sakamakon sanarwar da wasu matasan Arewa, suka fitar don hana sanatoci shiga kowacce jahar Arewa, tare da cewar matukar suka yi kunnen kashi suka shigo za su yi musu ruwan dutsuna kamar yadda jaridar observerstimes ta ruwaito .
Wannan ba zai rasa nasaba da fusatar da al’umar arewacin Nigeria suka yi ba, kan kudirin dokar sauya fasalin haraji, ake kallon jahar Lagos ce za ta fi cin moriyarta.
Sanata Barau, ya ce dan kare baki na gida da kasashen ketare, ya zama dole aka mayar da daurin auren zuwa birnin tarayya Abuja, aranar 13 ga watan Disamban 2024.
- Shugaban Jam’iyar APC Na Karamar Hukuma Gezawa Alhaji Sani Yamadi Ya Gwangwaje Daliban Da Suka Yi Sauka A Garin Jannarya Da Atamfofi.
- Wata Babbar Kotun Kano Ta Wanke Wata Dattijuwa Daga Zargin Kashe Yarinya Da Jefa Gawarta A Rijiya.