Kungiyar ACF Ta Yi Allah Wadai Da Matakin Dakatar Da Sanata Ningi Kan Zargin Cushen N3trn

Spread the love

Kungiyar tuntuba ta Arewacin Nigeria ( ACF), ta nuna bacin ranta a fili kan matakin da majalissar dattawan kasar ta dauka kan dakatar da Sanata Abdul Ningi, biyo bayan zargin cushen Tiriliyan uku da sanatan ya ce an yi a cikin kasafin kudin shekarar 2024.


Idan ba a manta jaridar idongari.ng, ta ruwaito mu ku cewa Ningi ya bayyana zargin chushen kudin a wata tattauna wa da ya yi da BBC Hausa, inda majalissar dattawan ta ce zargi ne da ba shi da tushe balle makama.

Kungiyar ACF , ta yi kakkausar suka kan matakin da cewa, kamata ya yi majalissar ta gudanar da bincike, maimakon dakatar da shi, ba tare da yi wa al’ummar Nigeria bayanin da za su amince da yan majalissar masu jajayen kujeru ba.

Sakataren kungiyar ACF, Fafesa Tukur Baba, ne ya bayyana haka ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jahar Kaduna.

” Maimakon daukar matakin dakatar da Ningi, kamata ya yi a kafa kwamitin wucin gadin na gudanar da bincike mai zurfi” ACF”.

Kungiyar ta kara da cewa, matakin dakatarwar ya yi sauri, domin ita kanta majalissar bata wadatar da al’ummar Nigeria rashin ingancin abunda Sanata Ningi Ya bayyana ba, kawai sun dauki matakin dakatar wa da kuma musanta zargin yin chushen.

Zargin yin cushe ba sabon abu ba ne, domin ko shekarar 2020 , a watan Oktoba, lokacin da tsohon shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya gabatar da kundin dokar kasafin kudin a gaban majalisar dattawa da ta wakilai, ya gabatar da naira tiriliyan 10.3 ne a cikin kudirinsa.

Kotu Taki Amincewa A Saki Bayanan Kaddarorin Buhari Da Jonathan

Real Madrid ta ci gaba da yin ɗare-ɗare a saman teburin La liga

Amma kuma a lokacin da ya sanya hannu a kudirin don ya zama doka a watan Disamba 2020, bayan nazarin majalisar dokokin kasar, ya sanya hannu ne a kan kudirin da ya kunshi jimlar naira tiriliyan 10.6, wato an samu karin da ya kai na naira biliyan 264.

Yan Nigeria dai tuni suka sanya ayar tambaya kan yan majalissun, bisa zargin fifita kansu wajen kasafce wani bangare na kasafin kudin shekarar 2024 a tsakanin su, duk da halin kuncin rayuwar da al’ummar Nigeria ke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *