Daga: Mujahid Wada Musa Kano
Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta bayar da tallafin buhunan shinkafa 109, ga kungiyar yan jaridu ta (Arewa Online journalist Forum) don rage mu su raɗaɗin rayuwa musamman a watan Ramadan mai alfarma.
Hajiya Fatima ta yi shura wajen ganin ta saka farin ciki a fuskokin Alummar Najeriya musamman arewacin Najeriya.
Hajiya Fatima ta kasance daya daga cikin jigo, a kamfanin mahaifinta Dangote, wadda ta yi koyi da kyawawan hali na mahaifinta Alhaji Aliko Dangote wajen kyautatawa marasa karfi.
Shugaban Kungiyar Arewa Online journalist Forum, Malam Barrah Almadany, ya mika sakon godiya ga Uwar marayu Hajiya Fatima Aliko Dangote, a madadin sauraran mambobin kungiyar, sakamakon tsayawar da ta yi na , tallafawa mabukata da kayan abinci a wannan wata na Ramadan.
Jaridar Idongari.ng, ta ruwaito cewa shugaban, ya bukaci ma su hannu da shuni, su yi ko yi da Hajiya Fatima Aliko Dangote wajen taimakawa mabukata don rage mu su radadi.
- Aliko Dangote Ya Kaddamar Tallafin Buhunan Shinkafa Na Sama Da Naira Biliyan 15 Ga Mutanen Nigeria Miliyan 1
- Gidauniyar Dangote Ta Raba Buhunan Shinkafa 1m A Nigeria, Da Ciyar Da Mutane 10,000 Kullum A Kano.