Kungiyar ASSOMEG Ta Taya Ibrahim Waiya Murnar Samun Kwamishinan Yada Labarai Na Jihar Kano

Spread the love

 

Kungiyar Mawallafa Jaridun Yanar Gizo ta The Association of Online Media Guild ASSOMEG ta taya Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya murnar nadin da aka yi masa na Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano.

 

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da shugaban riko na Kungiyar Abdullateef Abubakar Jos, da sakataren riko, Abbas Yushau Yusuf, suka ka fitar.

 

‘’Nadin Kwamared Waiya da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ya nuna jajircewarsa na tabbatar da dimokuradiyya, da shugabanci na gari,

A matsayinsa na Babban Darakta na kungiyar cigaban al’umma ta CDE kuma jagoranƘungiyar Kula da Al’ummar Jihar Kano Civil Society Forum (KCSF), ya kasance mai jan hankali wajen fayyace ka’idojin dimokuradiyya, yaki da cin hanci da rashawa, samar da zaman lafiya, da karfafawa jama’a gwiwa.

Sanarwar ta kara da cewa, ” ASSOMEG ta yi imanin cewa dimbin gogewar da Kwamared Waiya ke da shi da jajircewarsa ga aikin gwamnati zai taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa yada sahihan bayanai da suka dace a jihar Kano.

Nadin nasa wani muhimmin mataki ne na karfafa alaka tsakanin gwamnati da kafafen yada labarai.

‘’Muna sa ran hada kai da ma’aikatar yada labarai karkashin jagorancin Kwamared Waiya don ciyar da ka’idojin aikin jarida ta yanar gizo da kuma tabbatar da cewa ‘yan jihar Kano suna da masaniya kan manufofi da tsare-tsare na gwamnati.

“Har ila yau, muna mika sakon taya murna ga Kwamared Ibrahim Waiya bisa wannan mukami da ya cancanta da kuma yi masa fatan Allah ya saka masa da alheri.”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *