Kungiyar Atiku 2027 Network For Change Awareness ta kasa, karkashin jagorancin Hon. Ahmad Adamu Kwachiri Fagge, ta halacci taron kaddamar da shugabannin kungiyar a Jihar Nassarawa don ci gaba da wayar da kan jama’a kan cancantar tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Alhaji Atiku Abubakar da yake da ita don zabarsa a matsayin shugaban kasa.
Mai bayar da shawara kan harkokin Shari’a, Barista Ahmad Sani Bawa, ne ya bayyana hakan sakamakon nasarori da hadin kan da aka samu na yayin gudanar da taron.
Kungiyar Atiku 2027 Network For Change Awareness, ta ce daman kokarin wayar da kan jama’a Ake yi domin Alhaji Atiku AbubaKar, ba Bako ne ga Yan Nijeriya ba, domin babu Wani shugaba da ya yi saura a Nijeriya Sai shi, bisa rawar da ya taka a baya wajen gyara kasa da hidimtawa jama’a.
” idan Allah ya bashi dama Sai yafi dukkan Wadanda suka yi shugabanci a baya domin yasan damukuradiya”.
An kaddamar da shugabancin na Jihar Nassarawa a ranar Asabar 27 ga watan Satumba 2025.
Ahmad Sani Bawa, ya Kara da cewa an yi musu Karba ta musamman a jahar Nisarawar kuma komai ya gudana lafiya.
” wannan tafiya za ta ci gaba da gudana a jahohin Nijeriya 36, kuma za mu kaddamar shugabancin kafin lokacin da za a buga gangar siyasa” Ahmad Sani Bawa”.
Kungiyar ta ce kowa yaji a jikinsa a Yanzu kan halin matsi da kuncin rayuwa, don haka Yanzu babu Wanda yafi cancantar Zama shugaban kasa a 2027 Sai Alhaji Atiku AbubaKar, Saboda shi ne cikakken Dan siyasa Wanda yasan matsalolin Nijeriya.