Kungiyar Ci Gaban Unguwar Dukawuya Ta Yaba Wa Rundunar Yan Sandan Kano Wajen Dakile Aiyukan Batagari

Spread the love

 

Kungiyar ci gaban Unguwar Dukawuya dake Yankin karamar hukumar Gwale a jahar Kano ( Dukawuya Development Association), ta Kai wa Rundunar Yan Sandan jahar ziyara tare da bayar da Shawarwari kan matakan da suka dauka , a unguwarsu, don sauran al’umma su yi koyi da su, Wanda hakan zai taimaka  , musamman unguwannin da suke fama da aiyukan batagari a sassan birnin Kano.

Shugaban kungiyar, Alhaji Babagana Zanna , ne yabbaya hakan,inda ya ce cikin matakan da suka dauka sun hada da addu’a da kuma yin saukar karatun alku’arni, Mai tsarki a dukkan masallatan yankin da kuma taimakon juna ta hanyar daukara matasa a matsayin masu kula da  unguwar da daddare  tare da biyan su Wani Kaso na kudi a dukkan karshen wata.

” Wannan Alawus din da muke ba da ga ko’ina muke ba , a tsakanin mu domin mun dorawa kowanne gida kudin da zai bayar duk karshen wata kuma mutane suna taimaka wa ” Babagana Zanna “.

Ya kara da cewa, sun jawo matasan su jikinsu don lura da duk motsin da suke Yi, tare da Hana su yin banza Inda Ake koyar da su sana’o’in dogaro da Kai baya ga taimaka musu ta fannin Ilimi.

Ya Kuma ce wannan nasarar ta samu ne bisa Goyon bayan da masu rike da sarautun gargajiyar suke basu akoda yaushe.

Da yake nasa jawabin kwamishinan yan Sandan jahar Kano CP Salman Dogo Garba , ta bakin kakakin Rundunar Yan Sandan jahar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yayan kungiyar ci gaban Dukawuyan mutane ne masu kishin jahar Kano, bisa matakan da suka dauka sakamakon bibiyar wasu Abubuwa da suke faruwa a wasu unguwanni , Inda suka ga dacewa su gana da Yan Sanda don bayar da Shawarwarin hanyoyin da yakamata a dakile lamarin.

” Alhamdulillah mun gana da su, kuma Shawarwarin da suka bayar za mu Yi Aiki da su , domin Shawarwari ne masu kyau” SP Abdullahi Kiyawa “.

Haka zalika SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce bisa matakan da mutanen Dukawuyan suka dauka wajibi ne , sauran al’umma su farka ,don sanin wadanda suke zaune a unguwanninsu.

Kwamishinan Yan Sandan ya gode musu kan kokarinsu a harkar da ta shafi tsaro.

A karshe Rundunar taja hankalin al’ummar unguwanni su dinga duba matsalolin su don lalubo hanyoyin magance matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *