Kungiyar Daliban Yakasai Ta Kaddamar Da Wajen Koyar Da Dalibai Na’ura mai Kwakwalwa

Spread the love

 

Kungiyar Daliban Yakasai, wato Yakasai Students Association ( YAKSA) ta kaddamar wajen koyar da dalibai na’ura mai kwakwalwa,ya yin gabatar da taron da ta saba gudanarwa duk shekara, a unguwar dake yankin karamar hukumar birnin.

Shugaban kungiyar , kwamared Abdullahi Sabo NEPA, ya ce an bude wajen ne don ci gaban daliban Kano da kuma na Nigeria baki daya, duba da kalubalen da wasu dalibai ke fuskanta musamman ta yadda za su sarrafa na’urar.

ya ce za a koyar da matasan daliban don suma su dogara da kansu, duba da kalubalen rashin aikin yi da matasa ke fama dashi a fadin Nigeria, kuma duk abinda da za a koyar kyauta ne sai dai kudin Foam da mutum zai biya Naira 1,000, don daliban su ba wa abun muhimmanci.

Yanzu haka dai kungiyar ta samu kyautar na’ura mai kwakwalwa guda 25, daga hannun wasu masu ruwa da tsaki na unguwar ke tallafawa kungiyar ta bangarori daban-daban.

Mai unguwar Yakasai A, Kwamared Tajuddin Baba Yakasai, ya bayyana gamsuwarsa kan jajircewar daliban unguwarsa, da kuma burin gina wani babban abu da za a dade a morarsa.

Mai unguwar ya kara da cewa wannan wata hanyace ta yi matasa tarbiya, don jan hankalinsu musamman wajen dogaro da sana’o’in dogaro da kai.

Tsohon akanta general na kasa, Alhaji Ahmed Idris, na daga cikin manyan bakin da suka halacci taron, inda ya ba wa kungiyar kyautar naira dubu 250, sannan ya ba wa dukkan malaman da suke koyar da daliban naira dubu goma-goma.
Haka zalika ya ba wa wasu zakakuran daliban, da suka shiga musabakar karatun al’kur’ani, a wani bangare na taro suma naira dubu goma-goma.

Jarman Gaya, Alhaji Ibrahim BBY, ne ya samar da ginin cibiyar wajen koyar da daliban na’ura mai kwakwalwar, inda ya yi kira ga masu hannu da shuni, da su jajirce wajen taimawa al’umma.

Taron dai an gudanar da shi, a unguwar Yakasai Kano, a ranar Asabar inda ya samu halatar , masu rike da masarautun gargajiya, kungiyoyin dalibai, malamai da masu ruwa da tsaki na sassan unguwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *