Kungiyar kafafen yada labaran yanar gizo Association Online Media Guild ta taya gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf murnar yin nasara a kotun koli

Spread the love

Kungiyar kafafen yada labarai ta yanar gizo mai suna Association Online Media Guild, ta taya gwamnan jahar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf , murnar nasarar da ya samu a kotun koli.

A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa manema labarai ta hannun shugabanta na riko, Abdullateef Abubakar Jos da sakataren kungiyar, Abbas Yushau Yusuf, kungiyar ta bukaci gwamnan da ya yi amfani da nasarar wajen hidimtawa al’umma.

Idan dai za a iya tunawa kadaura24 ta rawaito, a ranar Juma’a nan ne Kotun Koli ta mayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamnan Jihar Kano bayan da kotun sauraren kararrakin zabe da kotun daukaka kara suka soke nasarar da ya samu a zabe.

Kungiyar yan jaridun ta yanar gizo ce ta tara yan jaridu da suke aikin su a yanar gizo daga sassa daban-daban na kasar nan, dake da hedikwata a Kano.

Kungiyar ta bukaci gwamnan jihar da ya kyautata kyakkyawar alakar da yake da ita da yan jaridun yanar gizo, domin Kano ce ta biyu da ta samu dimbin kafafen yada labarai na yanar gizo baya ga jihar Lagos.

Sun bukaci Gwamnan ya kara inganta tsare-tsaren da zasu ciyar da al’ummar jihar kano gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *