Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, ta ƙalubalanci ƴan majalisun ƙasa, waɗanda suka amince da ƙudirin dokar gyaran haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike wa zauren majalisar domin amincewa da shi.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar Kwamared Tasi’u Idris Idris (Soja) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da manema labarai a yau Lahadi, ya ce duba da tsananin rayuwar da al’ummar ƙasar nan suke ciki sam bai kamata shugabannin Arewa su amince da dokar gyaran harajin ba.
A ranar Alhamis ne dai ƙudirin dokar gyaran harajin ya tsallake karatu na biyu a zauren Majalisar Dattawa ta Najeriya, al’amarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, kuma daga cikin waɗanda suka nuna rashin amincewar su da dokar harajin har da sanatan Borno ta Kudu Ali Ndume, da gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zullum.
- Gwamnan Kaduna Uba Sani Ya Nada Sabon Kwamishinan Tsaro Bayan Sallamar Aruwan.
- Sojoji sun kashe jagoran Boko Haram Abu Shekau a Yob
A cewar Soja, “Ko kusa ko alama bai kamata ƴan majalisar Dattawa da na Wakilai su amince da ƙudirin gyaran dokar harajin ba, domin hakan ka ƙara kassara al’amuran Al’ummar arewacin ƙasar; muna kira ga shugabannin mu su kaucewa amincewa da dokar harajin domin ceto yankin su daga ƙangin ƙuncin rayuwa, “in ji Tasi’u Soja”.
Shugaban gudanarwar ƙungiyar ya kuma ce abin kunya ne kan yadda mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I Jibril, da sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga, da wasu shugabannin Arewa suka amince da ƙudirin dokar, domin ba abu ne da zai haifar wa Arewa Ɗa mai ido ba.
Tasi’u Soja, ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tunibu, da dukkanin shugabanni a Najeriya, da su dakatar da batun gyaran dokar harajin bisa yadda zai iya haifar da matsala a ƙasar.