Kungiyar ma su samarwa da sarrafa Zobo ta kasa ta bayyana farin cikin ta da ci gaban da ta samu wajen fitar da Zobo zuwa kasashen waje musamman kasar Maxico wadda abaya ta haramtawa Nigeria shigar da Zobo kasar.
Shugaban kungiyar ma su samar da Zobon reshen arewacin Nigeria, Alhaji Ibrahim Abdulkadir Jada, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da wani taro da kungiyar ta shirya a jahar Kano.
Alhaji Ibrahim Jada, ya bayyana irin alakar dake tsaninsu da manoman zobo da yadda suke gudanar da harkar tsakaninsu ta yadda ake sama wa matasa aiyukan yi da wannan sana’ar ta zobo.
karan ta wannan labarin Hukumar hisbah ta jahar Kano ta ce za ta ci gaba da kama ma su yada badala a Tiktok
karan ta wannan labarin Ba ni da masaniyar biyan masu sa ido a zaɓe $6m da Emefiele ya yi
Mai Magana da yawun kungiyar ma su zobon, Alhaji Auwal Bello Dabai, ya bayyana jin dadin sa da yadda kungiyar ta ke kara samun hadin kan mambobin a kowanne lokaci.
Taron ya samu halattar dinbum ma su sana’ar zobo na arewacin Nigeria, inda suka yi fatan samun ci gaban da yafi wanda suka samu.