Kungiyar Malaman jami’ar YUMSUK Sun Janye Yajin Aikin Da Suka Tsumduma.

Spread the love

Kungiyar Malaman jami’ar Yusuf Maitama Sule (ASUU) reshen jahar Kano, ta sanar da janye yajin aikin da ta tsunduma tun a Ranar 24 ga watan Mayu 2024.

Shugaban kungiyar Malaman jami’ar Yusuf Maitama Sule, Dr. Mansur Sa’id , ne ya bayyana hakan ta cikin sanarwar da ya aike wa jaridar , Idongari.ng.

Dr. Mansur , ya ce daman yajin aikin na su na gargadi ne , wadanda suka shafe makonni biyu suna Yi, kuma sun janye ne sakamakon majalissar dokokin jahar Kano ta shiga cikin lamarin.

Ya Kara da cewa, sun kuma gana da mai girma gwamnan jahar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, inda suka sanar da shi irin abubuwan da suke damu makarantunsu , dangane da kudin gudanar wa, Majalissar zartarwa ta jami’a, Karin albashi da kuma bashin da Malaman suke bi.

” Mai girma gwamna ya gano inda matsalar ta ke, don haka ya Yi alkawarin cewar za a gyara cikin mako guda”.

Dr. Mansu Sa’id , ya ce bayan tattaunawar da suka Yi da gwamnan jahar Kano, shi yasa suka zauna tare da janye yajin aikin, amma dai kusan kwanaki 12 kenan ba tare da gwamnatin ta aiwatar da daya daga cikin alkawarin da ta daukar mu su ba.

“Muna so mu sanar da mutane cewa mun dawo daga yajin aiki kuma muna fatan gwamnati za ta cika alkawarin ta, sannan za mu ci gaba da tuntubarsu” DR. Mansur”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *