Kungiyar Malaman Kwalejin Shari’a Ta Mallam Aminu Kano Ta Rufe Makarantar Bayan Dakatar Da Dalibai Rubuta Jarrabawa.

Spread the love

Ƙungiyar malaman kwalejin shari’a ta Malam Aminu Kano (Legal) ta dakatar da rubuta jarrabawar da dalibai ke yi tare da rufe makarantar.

Daukar matakin ya biyo bayan kalaman da kwamishinan ilimi mai zurfi Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya wallafa shafinsa na Facebook dake nuna rashin goyan bayan cire kalmar “Islamic” daga cikin sunan makarantar.

Cire kalmar dai na daga cikin ka’idojin da za’a cika kafin a daga likafar makarantar zuwa kwalejin ilimi wato College of Education.

Ga dai rubutan da kwamishinan yayi a sahihin shafinsa na Facebook;

 

MAKARANTAR LEGAL TA SAMU TAGOMASHI NA CIGABA, AMMA BAZAMU YARDA DA CIRE “ISLAMIC” DAGA SUNAN MAKARANTARBA

Mun samu wani ƙudiri da yunƙuri na wasu tsirarin mutane akan neman sai an cire kalmar “Islamic” daga sunan makarantar Legal mai tarihi da albarka- wato Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies (AKCILS).

 

Masu son a cire “Islamic” daga sunan sunyi proposing ta koma Aminu Kano College of Education and Legal Studies. A cewar su sai an cire kalmar “Islamic” ne, sannan zata iya komawa tsangayar ilimi, wato College of Education. Masu irin wannan tunanin, mafiyawancinsu basusan dalilin kafa makarantarba a shekara ta 1976 da kuma irin gudunmawar da ta bawa da addinin musulunci.

Da irin wannan mutanen ne a baya aka haɗa baki aka kassara makarantar ta hanyar sayarda gine-ginenta da filayanta ga marasa kishin Kano. Wasu tsirarin kuma, kunya suke ji ace sunan makarantarsu har da “Islamic” a ciki, saboda sunfi so aji sunan boko zalla a makarantar. Ba mamaki ko dan kwalinsu bai shafi ƙudurin makarantarba. Wasu kuma tunanin makomarsu suke, ba makomar ilimi a jihar Kano ba, yayin da wasu kuma suke ƙoƙarin siyasantar da ilimi.

Alhamdulillah, mun tattauna da mafi rinjaye daga cikin malamai da kuma manyan tsofaffin ɗaliban makarantar da masu hannu da shuni, kuma sun bayyana rashin amincewarsu da cire kalmar “Islamic” ɗin da wasu tsiraru suke ta ƙoƙarin kawar da ita daga sunan Legal.

Za mu cigaba da ƙoƙarin ganar dasu, da kuma ɗaukar matakai a gwamnatance. Sannan kuma, muna daɗa tabbatarwa da duniya cewa, makarantar Legal zata cigaba da ƙudurin da aka gina ta akai, sannnan kuma zamu cigaba da ƙoƙari don ta samu lasisin horar da malamai, ba tare da ancire “Islamic” a sunanta ba. Ma’ana, basai an cire sunan musulunci zata zama College of Education ba, kamar yadda wasu masu gajeren tunani suke hasashe.

Makarantar mai ɗinbin tarihi, ta taimaka wajen samar da manyan malamai, alƙalai, da masu faɗi aji a Kano. Sannan kuma ta taimakawa mutanen da sukayi karatun Alqur’ani ko Islamiya ta hanyar zamanantar da iliminsu, da kuma basu certificates a fannoni daban-daban.

Gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf bazata lamunci wani ƙudiri ba wanda zai salwantar da tarihi ko maida jihar baya.

Sannan ina sanar da jama’a cewa kowacce makaranta da dalilin da yasa aka kafata. To ya zama dole akiyaye dalilin kafata, a yayin da ake ƙoƙarin canja mata akala. Akwai abubuwa masu muhimmanci da nake shawartar malamai da kuma ƙungiyoyin makarantar su mayar da hankali akai, kamar kai ƙorafin kadarorinta da aka kwace wajen kwamitin da maigirma gwamna ya kafa domin jin ƙorafi da kuma kwatosu, wanda a halin yanzu yananan yana karɓar ƙorafa-ƙorafe na kadarorin gwamnati da aka salwantar. Duk mai kishin Legal to wannan abin ya fi kamata ya maida hankali a yanzu. A waje ɗaya kuma, zamu hada kai da hukumar makarantar don kwato kadarorinta.

Sannan kuma shiri yayi nisa don tabbatar da cigaban makarantar ta hanyar ƙarfafar Consultancy Directorate, Continuing Education, affiliations, gyaran dokar makarantar da sauransu. Zakuma mufarfaɗo da ƙudare-ƙudaren na makarantar na baya don samun nasarar ilimi a Kano. A yanzu haka muna magana da jami’ar Ummul-Qura dake Makka, domin inganta harshen larabci da kuma samun ƙudaden shiga. Sannan kuma shiri yayi nisa a makarantar domin fara digiri a fannoni guda hudu. Haka zalika duk ƴan kwangilar da suke aiki a makarantar, mun umarcesu da su koma bakin aiki. Zakuma mu duba yiyuwar samowa malaman makarantar guraben ƙara karatu a inda yakamata, musamman a sabon tsarin da muke shirin yi.

Mu kuma zamu cigaba da consultation ta hanyar tattaunawa da duk tsofaffin shugabannin makarantar da manyan ɗalibansu da kuma hukumar makarantar don kara kawo cigaba a makarantar. Masu kuma wancan tunanin, muna shawartarsu da su faɗaɗa tunani, su kuma zama masu kishin jiharsu da addininsu domin kaucewa ruɗin duniya.

Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata

Komishinan Ilimi Mai Zurfi

9th May 2024/Zulqidah 1st, 1445

Kadaura24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *