Kungiyar ( POWA) Reshen Jahar Kano Ta Fara Zagayen Rangadin Gana Wa Da Matan Yan Sanda Da Iyalansu.

Spread the love


Shugabar kungiyar matan yan sanda ( POWA) reshen jahar Kano, Hajiya A’isha Muhammed Usaini Gumel, ta fara ziyarar rangadi don gana wa da matan yan sanda tare da iyalansu, don tattauna wa da su kan kalubalen da suke fuskanta a Barikokin yan sanda dake jahar.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da jam’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

Sanarwar ta kara da cewa shugabar kungiyar POWA, ta ziyarci, sansanin rundunar yan sandan kwantar da tarzoma dake Hotoro, ofisishin kwamandojin yan sandan Metro da Hotoro da kuma Police Primary School.

Hajiya A’isha Gumel, ta saurari koke-koken matan yan sanda da kuma jami’an yan sanda mata, domin inganta wuraren zamansu da kuma wajen aikin jami’an yan sanda mata.

Haka zalika shugabar Powa ta ce, kungiyar  zata ci gaba da bayar da fifiko wajen tabbatar da tsaron lafiyar yayan kungiyar da samar da  muhallinsu da kuma taimaka mu su ta kowanne bangare.

Hajiya A’isha Muhammed Gumel

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *