Kungiyar POWA Ta Kammala Ziyarar Ganawa Da Matan Yan Sanda Da Iyalansu A Kano.

Spread the love

Shugabar kungiyar matan jami’an Yan Sanda reshen jahar Kano, Police Officers Wives Association (POWA), Hajiya Fati Dogo, ta kammala rangadin da ta kai, manyan ofisoshin Yan Sanda da kuma na kwantar da tarzoma a sassan jahar.

 

Kungiyar ta fara ziyarar, a ranar 26 ga watan Nuwamban zuwa 12 ga watan Disamba 2024, don duba wasu aiyuka, a barikokin Yan Sandan , da Iyalan Yan Sandan ke rayuwa, Inda ta tattauna da matan Yan Sanda da Iyalansu don tallafawa matan da suka rasa mazajansu a fagen daga.

 

Kakakin Rundunar Yan Sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce shugabar , ta ziyarci sansanonin Yan Sandan Metro, Tarauni, Kano Central, Dala , Eastern Bypass, Bichi, Danbatta, Rano, Tudunwada, Wudil da kuma sansanonin Yan Sadan kwantar da tarzoma guda biyu na Chalawa da Hotoro.

Rangadin ya bayar da damar tattauna wa Tsakanin shugabar kungiyar da matan Yan Sanda da kuma jami’an Yan Sanda mata, tare sauraren Abubuwan da suke damunsu da kuma Shawarwarin da aka bayar don Samar mu su zamantakewa Mai kyau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *