Kungiyar Rayuwa Development Association (RADA) Ta Kudiri Aniyar Nema Wa Matan Da Aka Ci Zarafin Su Mafita.

Spread the love

 

Kungiyar Rayuwa Development Association ( Rada ) ta gudanar Taron wayar da kan mata, a ci gaba da tunawa da ranar yancin dan Adam, sakamakon yawaitar Samun korafe-korafen cin Zarafin mata a birni da karya a sassan jahar Kano.

Wata Lauya mai zaman kanta, kuma mai rajin kare hakkin Dan Adam, barista Badiha Abdullahi Ma’az, ce ta jagoranci wayar da kan wasu daga cikin matan da aka ci Zarafinsu, don lalubo hanyoyin magance matsalar Baki daya, da kuma Nema wadanda aka Zarafinsu hakkokinsu ta hanyar Shari’a.

Barista Badiha Abdullahi, ta bayyana hakan ne ga Jaridar idongari.ng,  a birnin Kano.

A cewar lauyar ta shafe sama da Shekaru 15, ta na kokarin nema wa Yaya matan da aka ci Zarafinsu hakkokinsu saboda marasa karfi ne kuma wasu ba su ma san inda za su Kai koken na su ba.

Matukar ban shiga cikin shari’un marasa galihu ba, to akwai Shari’ar da adalcin ta ba zai taba bayyana ba, saboda ma su rangwamen gata ne.

” Shari’a ta zama kamar ta yada kanin Wani, ta zama sanaiya, ta zama arrangement, ta zama Kawai in baka da gata ko ba zaka iya daukar lauya ba to ba za a Yi da Kai ba sai Sa’a sai tsananin rabo” Barista Badiha Ma’az”.

Ta kara da cewa ganin yadda Ake gallazawa mata, ko cin Zarafi ba adadi balanta iyaka, Inda ta ga Abubuwa marasa dadi kuma ya Sanya ta a cikin damuwa da tashin hankali.

” Naga yar wata shaida an Yi mata fyade, naga yar shekaru shida an ci Zarafin ta, naga wadda ubanta ne ya Yi mata, naga wadda wanta ne , naga Kani, naga Mai uwa naga Abubuwa da yawa, idan naje na gansu na dawo sai na kidima , banda tunanin wai yaushe rayuwar Dan Adam ta koma haka”.

Ta ce a lokuta daban-daban, idan tana ba wa Mai gidanta Wani labarin har Kuka yake Yi, sannan ita kuma saboda zafin abun har zazzabi ta ke Yi saboda kidima.

Dangane da hakan ne Mai gidan nata ya ba ta shawarar su kafa kungiya, kuma yanzu haka sama da Shekaru 15 suna tafiyar da ita.

Ta kuma bayar da misalai kan yadda taje kotu ta tarar da wata mata da mijinta ya ce ba yarsa ba ce saboda zafin rabuwar da suka yi a matsayin su na ma’aurata, Amma bayan sun shiga cikin lamarin ya amince shi kuma aka kai shi gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.

 

Haka zalika akwai wata mata da ta ranci kudi naira Dubu dari da hamsin, a wajen wata mata don yin cikon kudin maganin yarta , Amma matar da aka ranci kudin ta Yi mata karin kudin ruwa ya koma naira Miliyan Daya da naira Dubu Talatin, Wanda hakan ya sa ta Yi zaman gidan yari kwanaki 45, Kafin lauyar ta shiga cikin maganar, Inda yanzu haka Ake ta kokarin biyan kudin, Matar tana zuwa kotun daga Yanshana na karamar hukumar Kumbotso zuwa Dawakin Kudu, a karamar hukumar Dawakin Kudu, a kasa , wadda take fitowa daga gida tunda sallar Asuba sannan ta isa kotun karfe 10 na safe, Inda jami’an kotun suke siya mata abinci.

Sannan akwai wata matashiyar budurwa da aka ci Zarafin ta tun tana da Shekaru 14, inda mahaifiyarta , ta koreta har fada Hannun wani soja Dan ya taimaka mata, Amma ya dinga yin Lalata da ita har ta samu ciki ta kuma haife danta namiji, sai dai ya ce ba Dansa ba.

 

Wannan takaddama ta Sanya an Yi gwajin Jini da ya dauki tsawon watanni 8 sannan ya fito , kuma binciken ya nuna cewa ba dansa bane.

 

Sai dai lauyar ta Yi Zargin cewa, an Yi amfani da damar da Allah ya ba wa wasu mutane kan wadanda basu da komai da kowa sai taimakon Allah.

 

Yanzu haka dai mutum na farko da Ake Zargin ya ci Zarafin budurwa, ya shigar da karar ta gaban kotu, da Zargin wai tana bata masa suna, bisa mazauna unguwarsu da suke cewa Dansa tunda an San abinda ya aikata mata.

 

Baristar ta kuma ce dukkan irin wadannan cin Zarafin da aka samu za su sake karkade takaddunsu don nemar mu su hakkokin su.

 

” Yanzu kunji abunda ya Faru, idan da zan dauko matan da aka ci Zarafinsu yau Taron nan gidan kuka zai koma, kuma sai naga duk lokacin da Taron nan ya tashi , sau Daya a shekara in as ka Yi buu ya tashi kamar kana koma toka ko hayaki, in akai wannan gangamin aka yada ya Wuce shikenan kuma Maimakon abun ya ragu karuwa yake”.

 

” Na zauna na Yi nazari sosai , Inda nago cewa rabuwar ma’aurata ne yake haifar da hakan sai tarbiyar Yara ta shiga Wani hali.

 

“Sannan suturar al’umma ita ce aure, ta aure Ake Samun iyali , yanzu iyalinnan idan an samu ba a farin ciki da ita , to Ina Annabi Muhammad Sallahu Alaihim Wassalam zai Yi farin ciki damu?”

Barista Badiha Abdullahi, ta ce don Samun mafita shi ya ta Nemo wadanda aka Zarafinsu, kuma marasa galisu don fidda mafita da za ta amfanar da su.

 

” Idan muka hada Kai da ku Yan Jarida da Wadanda aka ci Zarafinsu za samo mafita, wajen tallafa musu kuma mubi bayan tallafin” Barista Badiha”.

 

A karshe ta ce za su sake daukar bayanan wadanda aka ci Zarafin su don sake koma gaban kotu.

 

Hajiya Waji’ha Abdullahi Ma’az, Malama ce a jami’ar Ahmadu Bello Zaria ( ABU), ta bayyana makasudin shirya Taron, da cewar a matsayin su na mata lokaci ya Yi , da za su dinga dogaro da kansu , ta hanyar yin sana’o’i Koda a cikin gidajen aurensu.

Ta kara da cewa akwai noman zamani Wanda mace Koda tana cikin gidan ta zata iya nomawa don magance yawan cin Zarafin mata.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *