Kungiyar tsofaffin daliban makaranta faramaren Gandun Albasa a karamar hukumar birni Kano, ta gudanar da Taron sada zumunci da taimakon makarantar.
Shugaban kungiyar comrade Mukhtar Sulaiman Bello ya ce wannan taron shene karo na farko da yahada tsofaffin malamai dakuma daliban dasuka kammala a lokacin, inda bayyana cewa zasu ci gaban da taimakon makarantar da kayan koyo da koyar wa harma da taimakon tsoffin malamai.
Da yake jawabi a wajan taron tsohon shugaban makarantar mallam Habib Muhammad Dausayi ya yaba wa tsofaffin daliban akan kokarin da suke yi wajan taimakwa makarantar da kuma sada zumunci a tsakaninsu.
Kazalika shugaban makarantar na wannan lokaci wada malan Salisu Muhammad ya wakilta bayyana kalubalen da makarantar ta ke fuskanta da kuma kira ga mahukunta domin kawo daukin.
Daga karshe guda daga cikin tsofaffn daliban makaranta Amina Abdullahi Imam ta bayyana gudiyar su ga malamai da kuma jagororin da suka ba su ilimi da tarbiya har suka Kai matsayin da suke kai.