Kungiyar Tsofaffin Daliban Tsangayar Koyar Da Harsuna Na Jami’ar SRUOE, Ta Kaddamar Da Sabon Shugabancin Rikon Kwarya.

Spread the love

Kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kano, aji na 2015, sashin Turanci da Hausa dake tsangayar koyar da harsuna, ta gudanar da taronta karo na 7 da ta Saba yi duk shekara, don sada zumunci da taya juna murnar barka da sallah.

Shugaban kungiyar tsoffin daliban na rikon kwarya, Aminu Umar Getso, ne ya shaida wa jaridar idongari.ng, hakan a wani bangari na gudanar da taron da aka gudanar a Ranar Lahadi.

Aminu Umar Getso, ya ce tun bayan da suka kammala karatun su a shekarar 2015, suka kafa kungiyar domin sada zumunci a tsakanin su da kuma Yi wa abokan karatunsu wadanda suka rasu addu’o’i.

Getso ya Kara da cewa a kowacce shekara suna da tsare-tsare da suke fitar wa don taimaka wa harkar ilimi da kuma marasa karfi dake cikinsu da ma daidaikun jama’a.

Ya ce kudin da suke yin aikace-aikacen sune suke samar wa a junansu kowacce shekara don bayar da gudunmawar da za ta amfanar da al’umma.

” A shekarun baya munbi makarantu kakana , inda muka Gyara mu su Bandakuna , Kujeru da kuma kayan karatu da rubutu” Getso”.

Haka zalika kungiyar ta samarwa da marayu kayan makaranta da ba su kayan koyo da koyarwa don su samu ilimi kamar Kowa.

Sai dai ya ce a wannan shekarar sakamakon matsin tattalin arzikin da ake fuskanta, gidauniyar kungiyar ta tallafawa marasa karfi a cikin kungiyar har su biyar da naira dubu ashirin-ashirin kowannensu.

A karshen taron Kungiyar tsofaffin daliban jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi Kano, aji na 2015, sashin Turanci da Hausa, ta kaddamar da sabon shugabancin rikon kwarya.

Aminu Getso
*CHAIRMAN*

Yusuf Musa Memai
*VICE CHAIRMAN I*

Salwa Muhammad Ɗannagari
*VICE CHAIRMAN II*

Adam Umar Abdullahi Yakasai
*SECRETARY*

Ɗanladi Garko
*ASST. SECRETARY*

Mudassir Sabo Sa’id
*TREASURER*

Salisu Makoda
*FINANCIAL SECRETARY*

Abubakar Yahaya Makama
*WELFARE I*

Halima Isma’il
*WELFARE II*

*PRO’S TEAM*
1. Mujahid Wada Musa
2. Sulaiman Kabiru Isah
3. Muhd Jamil Yusuf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *